Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya amince da nadin mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya OON, a matsayin wanda zai jagoranci aikin hajjin bana wato ‘Amirul Hajji’ na 2023.
Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Ibrahim Muhammad Kashim, shi ne wanda ya sanar da nadin na gwamnan, ya shaida cewar nadin kuma zai fara aiki ne nan take.
- Da Dumi-Dumi: Sanata Abdul Ningi Ya Lashe Zaben Sanatan Bauchi Ta Tsakiya
- Kauran Bauchi Zai Gyara Kasuwar Katako Da Gobara Ta Kone Da Tallafin Miliyan 10
A cewarsa, nadin Alhaji Danyaya da sauran muhimman mambobi su 24 ‘yan asalin jihar da za su kasance a tawagar, an yi ne bisa kyakkyawar tarihinsu da aikinsu tukuru, himma, kwazo, kishin kasa, rikon amana, jajircewa da kuma tsohon Allah dinsu.
Bala ya bukaci mambobin tawagar da su yi aiki tukuru wajen sauke nauyin da ke kansu tare da tabbatar da sun gamsar da irin yardan da gwamnati da al’ummar jihar suka musu.
Kamar yadda Malam Mukhtar Gidado, kakakin gwamnan jihar, ya fitar ta cikin wata sanarwa a daren jiya Juma’a, ana sa ran tawagar Amirul Hajjin za su yi aiki kafada-da-kafada da hukumar jin dadin alhazai ta jihar, da sauran hukumomin da lamarin ya shafa na jiha, kasa da ma kasashen waje domin tabbatar da an gudanar da aikin hajjin bana cikin kwanciyar hankali da nasara.
Kazalika, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Rt. Hon. Danlami Ahmed Kawule shi ne zai kasance mataimakin Amirul Hajjin a bana.
Sauran mambobi sun hada da: Mai shari’a Rabi Talatu Umar, babban jojin jihar Bauchi; Hon. Khadi Umar Liman Grand Khadi na jihar Bauchi; Imam Bala Ahmed Baban Inna, babban limamin Bauchi; Hon. Tijjani Mohammed Aliyu, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Bauchi; Hon. Bakoji Aliyu Bobbo, shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar; Hon. Bala Abdullahi Dan na BAHA.
Saura su ne: Hon. Umar Babayo Kesa, kwamishinan ma’aikatar harkokin addinai; Hon. Abdulrazak Nuhu Zaki, kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya.
Sauran mambobin sun kunshi: Alhaji Ibrahim Y.M. Baba, Sarkin Duguri; Alhaji Aliyu Yakubu Lame, Sarkin Yakin Bauchi; Alhaji Bala Sulaiman Adamu, Dan Galadiman Bauchi; Alhaji Iliyasu Aliyu, Hakimin kasar Akuyam; Alhaji Umar Ibrahim, Sarkin Shira; Alhaji Yayanuwa Zainabari, sakataren watsa labarai na PDP a jihar Bauchi; Sheikh Salisu Sulaiman Ningi; Barista Garba Hassan; Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi; Malam Mustapha Baba Ilelah, shugaban hukumar shari’a ta jihar Bauchi; Alaramma Zakari Ya’u Dan-Yusuf Dauduwo; Ahmed Inuwa Na’ibi, mataimakin babban limamnin Bauchi da Alhaji Bala Hadith jigo a jam’iyyar PDP.
A fadin sanarwar, Yahaya Abubakar Umar shi ne zai yi aiki a matsayin sakataren tawagar Alhazan yayin da kuma Aliyu Adamu Abdulkadir zai yi aiki a matsayin mataimakinsa sakataren.