Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya miƙa ta’aziyyasa bisa rayuwar fitaccen malamin addinin Muslunci a jihar, Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi wanda ya rasu a ranar Alhamis bayan fama da rashin lafiya.
Gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ke misalta rashin a matsayin babban rashi tare da jajanta wa almajiransa da iyalansa bisa wannan rashin.
- EFCC Ta Cafke Mutum 21 Bisa Zarginsu Da Zambar Intanet A Bauchi
- Kamun Akanta-janar Take-taken Toshe Bakin Gwamnan Bauchi Ne – Ƙungiya
Ya ce: “Cikin alhini tare da fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki, mun wayi gari da rasuwar ɗaya daga cikin malaman addinin Musulunci daga nan jihar Bauchi, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, bayan fama da jinya.
“Yayin da muke roƙa masa gafarar Allah maɗaukakin Sarki, a madadin ni kaina, iyali gwamnati da ɗaukacin al’ummar Bauchi, ina isar da ta’aziyya ga iyalan marigayi Malam da almajiransa.
“Allah ya ba mu haƙurin juriya, ya haskaka kabarin sa.
“Idan ajali ya riske mu, ya Allah ka sa mu cika da imani, Amin,” Gwamna ya shaida.
Tunin dai aka yi sallar janaza ga mamacin tare da kaisa makwancinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp