Gwamnan Jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, ya sallami dukkanin masu rike da mukaman siyasa.
Wannan bayanin na kunshe ne ta cikin sanarwar da sakataren Gwamnatin jihar, Foluso Daramola ya sanya wa hannu tare da raba wa ‘yan jarida a Ado-Ekiti a karshen mako.
Wannan matakin na bisa tsarin dokar mika mukii a jihar ne da kuma tabbatar da an biya dukkanin masu rike da mukaman siyasa hakkokinsu bisa hidimar da suka yi.
Daramola ya kara da cewa gwamna Fayemi ya amince da dakatar da nadin hadiman ne da zai fara aiki daga ranar 31 ga watan July 2022.
Ya ce, wannan matakin an yi domin gwamantin jihar ta samu cikakken damar biyan jami’an dukkanin hakkokin da suke bi domin tabbatar da shirye-shiryen sauya gwamnati ya gudana cikin kwanciyar hankali.