Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya kafa doka mai lamba 8 ta 2024, da nufin tsaurara matakan sanya ido da kuma daidaita harkokin hakar ma’adanai a fadin Jihar Gombe don kare al’ummomin da ake hako ma’adanan a cikinsu daga cin zarafi da kuma kare muhalli.
Dokar wacce ta fara aiki nan take, za ta magance kalubale daban-daban da hakar ma’adanai ke haifarwa, wadanda suka hada da lalata muhalli da haddasa matsalolin tsaro da cin zarafin al’ummomin da ake hako ma’adanan a cikinsu.
- Sin Ta Kulla Yarjejeniyar Tsarin Kafa Huldar Abota Ta Raya Tattalin Arziki Cikin Hadin Gwiwa Tsakaninta Da Kasashen Afirka 22.
- Me Ya Haddasa Cacar Baki Tsakanin Kwankwaso Da PDP?
Muhimman abubuwan da suka shafi dokar sun hada da kafa kwamitin sanya ido kan ayyukan hako ma’adanai (MAMC), wanda kwamishinan makamashi da ma’adinai ke jagoranta.
Kwamitin ya kunshi wakilai daga ma’aikatu da hukumomin tsaro daban-daban, da Hukumar Zamanantar da Harkokin Filaye ta Jihar Gombe (GOGIS). Kwamitin yana da alhakin kula da duk wasu harkokin hakar ma’adinai a jihar, da tabbatar da bin dokoki da kuma hada kai da hukumomin gwamnatin tarayya don rage matsalolin muhalli.
Wani muhimmin al’amari na dokar shi ne, yadda ta bukaci duk kamfanonin hako ma’adanai su mika takardar yarjejeniyar amincewa da ta ci gaban al’ummar da za a hako ma’adanan a yankinsu zuwa ga ma’aikatar shari’a ta jihar ta hannun ma’aikatar makamashi da ma’adinai don tantancewa kafin fara duk wani aiki na hako ma’adanan.
Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli a wata sanarwar da ya fitar, ya ce, wannan matakin zai tabbatar da ana gudanar da ayyukan hakar ma’adanan daidai da muradun al’ummomin da ke wurin da kuma tabbatar da cewa duk yarjeniyoyin sun samu sahalewar doka.
Haka kuma, dokar ta ba da umarnin cewa duk ma’aikatan kamfanonin hako ma’adinai da suka zo Jihar Gombe, dole ne kwamitin na MAMC ya tantancesu don tabbatar da su ko suna da takardun izinin zama a Nijeriya, da ma matsayinsu a fuskar shari’a.
Haka kuma dokar ta zayyano irin rawar da hukumar tattara kudaden shiga ta Jihar Gombe (GIRS) da kananan hukumomi za su taka wajen karbar haraji da kudaden shiga daga kamfanonin hako ma’adanai a jihar.
Kwamitin na MAMC tare da hadin gwiwar wadannan hukumomi ne ke da alhakin tabbatar da bin umarnin bincike da gurfanar da duk wadda aka samu da karya dokar.