Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna alhininsa da kaduwa bisa samun labarin rasuwar malamin addinin musulunci a jihar kuma daya daga cikin mambobin hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar, Sheikh Abdulrahman Umar Maigona da ya rasu a kasa mai tsarki ta Saudiyya.
Sheikh Maigona ya rasu ne a ranar Alhamis a Makkah da ke kasar Saudiyya Arabiyya a matsayinsa mahajjaci.
- 2023: INEC Za Ta Rufe Rajistar Katin Zabe A Karshen Watan Yuli
- Tattalin Arzikin Kasar Sin Yana Kara Daidaita
A wata sanarwar da daraktan yada labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe Malam Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya nuna matukar kaduwa da jijjiga bisa rasuwar malamin, ya misalta marigayi babban limamin masallacin Izalah mai lamba 8 a matsayin hazikin malami da ya yi rayuwa abin koyi kana ya kwashe tsawon shekaru yana koyar da ilimin addini da dora mutane bisa tafarkin Allah da sunnar Manzon (SAW).
Inuwa ya ce, rasuwar malamin babban gibi ne ba kawai ga zallar iyalansa ba har ma da illahirin jihar da kasar nan baki daya.
Daga nan sai gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai, al’ummar jihar Gombe, abokai ciki har da ministan sadarwa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, hukumar gudanarwa da ma’aikatan Jami’ar jihar Gombe, inda marigayin yake a matsayin Malami a tsangayar da ilimin addinin musulunci tare da mika jaje ga illahirin al’ummar musulmai na jihar.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin ya gafarta masa dukkanin kura-kuransa kana ya sanya shi cikin Aljanna Madaukaka wato ‘Aljannat Firdaus’.
Idan za ku iya tunawa dai mun ba ku labarin da ke cewa Sheikh Abdur-Rahman Maigona, ya rasu ne a kasar Saudiyya sa’ilin da ke aikin hajjin bana a can.