ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Gombe Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Da ‘Yan Daba Suka Yi Wa Amadi Kasiran

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
6 months ago
gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kakkausar suka da Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wani matashi dan shekaru 45, Ahmed Aliyu, wanda aka fi sani da Amadi Kasiran, inda wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai masa hari tare da kashe shi a unguwar Hammadu Kafi da ke Gombe.

Mummunan lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadin da ta gabata, inda aka cakka wa marigayin wuka, kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa a asibitin kwararru na Gombe, kamar yadda rahotannin tsaro suka tabbatar.

  • Bukatar Kara Yawan Masu Fitowa Kada Kuri’a A Zabuka Nan Gaba
  • Yadda Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Zame Wa Nijeriya Alakakai

Da yake tsokaci kan lamarin, Gwamna Yahaya ya nuna bacin rai da alhininsa, inda ya bayyana kisan a matsayin rashin hankali, kuma abin da sam ba za a lamunta ba.

ADVERTISEMENT

Ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da sake dawowar aika-aikar ‘yan kalare da ‘yan daba a Gombe ba, kamar yadda kakakinsa Ismala Uba Misilli ya fitar ta cikin wata sanarwa.

“Wannan mummunan aika-aika ne kai tsaye ga zaman lafiya da tsaron al’ummarmu, a sani, tashin hankali ba shi da gurbi a Jihar Gombe, kuma za mu sanya kafar wando daya da duk wanda aka kama yana tada zaune tsaye,” in ji gwamnan.

LABARAI MASU NASABA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Ya umurci jami’an tsaro su gaggauta kai dauki ba tare da bata lokaci ba don tabbatar da an gurfanar da masu laifin a gaban kuliya, yana mai jaddada cewa za a hukunta duk wanda aka samu dauke da muggan makamai ko kuma aka samu yana da hannu wajen aikata laifuka.

“Ga iyalai da ‘yan uwa da masoyan marigayi Ahmed, ina mika sakon ta’aziyyata, da na gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, kuma muna jimami tare da ku, ina ba ku tabbacin za a yi adalci.

“Ina kuma kira ga jami’an tsaro su kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma sintiri kan tituna, musamman a wuraren da ke fuskantar irin wadannan laifuka. Jama’armu sun cancanci tafiya cikin walwala ba tare da tsoro ko barazana ga rayuka da dukiyoyinsu ba.

“Muna ci gaba da jajircewa wajen kare kowane rai da kuma tabbatar da cewa zaman lafiya da tsaro sun ci gaba da wanzuwa a wannar jiharmu.”

Ya yi kira ga al’umma su tallafa wa jami’an tsaro ta hanyar ba su bayanai masu muhimmanci kan lokaci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Next Post
Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.