A wani muhimmin mataki na ƙarfafa fannin ilimi da kuma girmama jajircewar aiki , Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da ingantattun sharuddan aiki ga malamai a faɗin jihar.
Gwamnan yace daga ranar 1 ga Agusta, 2025, an ƙara shekarun ritaya ga malamai daga shekara 60 zuwa 65, yayin da adadin shekarun hidima kuma ya ƙaru daga shekara 35 zuwa 40.
- Sin Za Ta Fadada Bude Kofarta A Fannin Ba Da Hidima
- Mujallar “Science”: Kasar Sin Tana Jagorantar Sauyin Salon Makamashi A Duniya
Bugu da ƙari, malamai da aka tura zuwa yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa za su rika karɓar alawus na musamman na aikin karkara.
Wannan amincewar ta yi daidai da Dokar Daidaita Shekarun ritaya ga Malamai a Nijeriya ta 2022, wadda Majalisar Tarayya ta kafa, wacce ta keɓe malamai daga ƙa’idar ritayar ma’aikatan gwamnati ta shekara 60 ko shekaru 35 na hidima, bisa la’akari da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ci gaban ƙasa.
A wata sanarwa da wamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Alhaji Ahmed Maiyaki, ya rabawa manema labarai ya ce wannan mataki yana nuna ƙudurin Gwamna Uba Sani na inganta walwalar ma’aikata da farfaɗo da fannin ilimi.
Ya bayyana cewa Gwamnan na ganin gogaggun malamai a matsayin ginshiƙi wajen samar da ingantaccen ilimi da ci gaba da kyakkyawan sakamakon koyo a duk faɗin jihar.
A cewarsa “Wannan manufa an tsara ta ne domin girmama shekaru na sadaukar da kai, riƙe ƙwarewa mai matuƙar amfani a cikin ajujuwanmu, da kuma ƙarfafa ƙwazo da aiki tukuru domin amfanin ’ya’yanmu da makomar Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.
Hakazalika, a wata takardada aka fita daga Ofishin Gwamna mai ɗauke da wannan amincewa, wadda Babbar Sakatariya ,Felicia I. Makama, ta sanya wa hannu, tare da umartar dukkan hukumomin da abin ya shafa da su bi umarnin.
Takardar ta ƙara da cewa Hukumar Kula da Ayyukan Gwamnatin Jihar za ta fitar da cikakkun ƙa’idojin aiwatarwa nan gaba kaɗan.
Gwamna Sani ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa wannan manufa za ta ƙara wa malamai ƙwarin gwiwa, ta inganta riƙon ma’aikata, tare da ɗaga matakin ilimi sosai a faɗin Jihar Kaduna, a matsayin wani ɓangare na ƙudurin gwamnatinsa na ƙarfafa cibiyoyin gwamnati da zuba jari a ci gaban ɗan Adam.














