Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya taya Al’amin Muhammed Idris, Shugaban Kamfanin (Interface Africa) kuma ɗan asalin Jihar Kaduna, murna bisa samun nasarar zama gwarzonsa gasar ƙirƙire-ƙirƙire ta duniya ta 2025 (NextGen Innovation Challenge) da aka gudanar a birnin Landan.
Wannan gasa ta ƙirƙire-ƙirƙire ta duniya, wadda Hukumar Ci gaban Fasaha ta Ƙasa (NBTI) tare da haɗin gwiwar kamfanin (UKALD) suka shirya, ta jawo mahalarta sama da 3,000 daga sassan Nijeriya, inda mutum 105 ne kawai suka kai ga zagaye na ƙarshe.
- Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba
- Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima
Kirkirar Al’amin mai suna (Interface Africa) wani sabon tsarin fasahar makamashi ne mai tsafta wanda ke haɗa masu samar da hasken rana, masu zuba jari da masu amfani da makamashi don faɗaɗa damar samun wutar lantarki mai saukin kudi ta hanyar shirinsa wacce ke da ɗimbin wakilai masu aikin samar da hasken wuta ga dubban gidaje.
An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka.
Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama.
“Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” in ji Gwamna Uba Sani.
“Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar kirkire-kirkiren Afirka,”
Gwamna Sani ya kuma jero wasu muhimman shirye-shirye da gyare-gyare na gwamnatinsa, kamar su Majalisar Kirkira da Fasaha ta Kaduna (Kaduna Innovation and Technology Council), Shirin Makarantun Zamani da Koyon Fasahar Zamani (Smart Schools and Digital Learning Programmes), da Kafa Cibiyoyin Koyon Sana’a da Fasaha uku a fadin jihar Kaduna