Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane shida (6) ga majalisar dokokin jihar domin tantance su a matsayin kwamishinonin ma’aikatu shida.
Wannan matakin dai ya biyo bayan sauya-sauyen da gwamnan ya yi a ƙunshin majalisar zartarwar tasa, inda aka cire wasu daga cikin mambobi, yayin da wasu ke rike da mukamansu wasu kuma an sauya musu ma’aikatu.
- Fahimtar Damammakin Da Sin Za Ta Samar Wa Duniya A Shekarar 2025 Daga Babban Taron Ayyukan Tattalin Arzikin Kasar
- Gwamna Abba Ya Umarci Kwamishinonin Da Ya Sauyawa Ma’aikatu Su Fara Aiki A Ranar Talata
Sunayen da aka miƙa a matsayin kwamishinonin domin tantancewa sun haɗa da; Alh. Shehu Wada Sagagi, Alh. Abdulkadir Abdulsalam da Ibrahim A. Waiya da Dr. Isma’il Danmaraya da Dr. Ghadafi Sani Shehu da Dr. Dahir M. Hashim.
Sauye-sauyen ya kuma bar wasu ma’aikatu da dama da suka haɗa da; Ci gaban Karkara da Kudi da Muhalli da Yada Labaru, Al’amuran jin kai da Wutar Lantarki.
Yanzu dai majalisar dokokin jihar za ta duba waɗanda aka naɗa domin tantancewa.