Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin a kamo tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, bisa zargin yunƙurin haifar da tashin hankali a jihar.
A daren jiya ne dai tsohon Sarkin ya shigo cikin birnin Kano a yunƙurinsa na komawa fadar mulkin Kano da ƙarfi da yaji bayan kwana biyu da Gwamna ya sauke shi a cewar Sanusi Bature Dawakin mai magana da yawun gwamnatin Kano.
- Gwamnatin Kano Za Ta Saya Wa ‘Yan Majalisar Jihar Motocin Naira Biliyan 2.7
- Zan Gaggauta Rattaba Hannu A Hukuncin Wanda Ya Kone Mutane A Masallaci – Gwamnan Kano
A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin Kanon Dawakin Tofa ya fitar, an tabbatar da cewa sabon sarki Sanusi Lamido Sanusi ya isa fadar ne tare da gwamnan jihar da mataimakin gwamna da kakakin jihar da ƴan Majalisar Kano da sauran manyan jami’an gwamnati da misalin ƙarfe 1:00 na daren Asabar, 25 ga Mayu, 2024.
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce; A matsayin gwamna na babban jami’in tsaro na jihar, ya umurci kwamishinan ƴansanda da ya kamo Sarki Aminu Ado da aka tsige ba tare da bata lokaci ba, saboda yunƙurin tada hankalin al’umma.