Duk da kokawar da wasu masu fashin baki ke yi kan wasu aikace-aikace da gwamnatin Jihar Kano ke yi da ake ganin ba su Kanawa suka fi bukata ba, sai aka wayi gari gwamnatin Kano ta amince da kashe naira biliyan 2.7 wajen saya wa ‘yan majalisar dokokin jihar motocin alfarma.
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya amince da kasha kudaden domin sayen motocin alfarma wadda kowacce daya ake sa ran za ta kai naira miliyon 68.
- Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Kano Ta Rushe Masarautun Da Ganduje Ya Kirkiro
- Jami’ai Sun Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Karkashin Dandalin FOCAC
Kamar yadda aka sani majalisar dokokin Jihar Kano na da mambobi guda 25 na jam’iyyar NNPP, yayin da guda 15 kuma na jam’iyyar APC, sai kuma guda daya da har yanzu ake jiran sakamakon matsayinsa.
Da yake karin haske kan lamarin ga manema labarai, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan majalisar dokokin sun cancanci samun nagartattun motocin aiki.