Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2025 na Naira biliyan 549.1 ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, wanda ya kira “Kasafin Gatan Jama’a, Gina Ɗan Adam da Tattalin Arziki.”
Wannan kasafi ya fi mayar da hankali kan fannonin jin daɗin jama’a da tattalin arziki, inda aka tsara kashe Naira biliyan 312.6 a matsayin manyan ayyuka da kuma Naira biliyan 236.5 don kuɗin gudanarwa, wanda ke nufin kaso 57:43 tsakanin manyan ayyuka da kudin gudanarwa.
- Gwamnatin Tarayya Ta Soke Kwangilar Gyaran Titin Abuja Zuwa Kaduna Da Kano
- Zanga-zangar Tsadar Rayuwa: Yaran Kano Za Su Shafe Kwanaki 5 A Asibiti Don Kula Da Lafiyarsu
An ware kaso 31% na kasafin (Naira biliyan 168.3) ga ɓangaren Ilimi, sai Lafiya da ke da kaso 16.5% (Naira biliyan 90.6), da kuma hanyoyi da ke da kaso 12.8% (Naira biliyan 70.7). Sauran ɓangarorin sun haɗa da Noma (3.8%), Gwamnati (17.5%), Tsaro da Shari’a (4%), da kuma ci gaban karkara (4.9%).
Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin ƙara jari a ɓangaren ilimi da manyan aiyuka don samar da ilimi ga kowa, rage talauci, da inganta samar da ayyukan yi. Ya buƙaci majalisar ta hanzarta amincewa da kasafin, yana mai shaida ƙudirinsa na ci gaban al’ummar Kano.