Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya gargaɗi malamai da su daina tilasta wa ɗalibai yin aiki mai wahala a makarantu ko wajen makaranta.
Sanarwar da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Lahadi ta bayyana cewa makarantu wurare ne na ilmantarwa da tarbiyya, ba na aiki da wahala ba.
- Mummunan Hatsari Ya Kashe Mutane 23, Da Yawa Sun Jikkata A Kano
- A Karon Farko An Zabi Mace Shugabar ALGON A Kano
Gwamnan ya yi wannan gargaɗi ne bayan wata ziyarar bazata da ya kai makarantar School for Arabic Studies a Kano, inda ya tarar da ɗalibai suna tona bututun ruwan bayan gida. Duk da cewa shugaban makarantar ya ce an ba su aikin ne bayan kammala karatu, gwamnan ya jaddada cewa hakan ba za a lamunta da shi ba.
A matsayin matakin gyara, Gwamna Yusuf ya bada tabbacin gyara duk gine-ginen makarantar da suka lalace, ciki har da masallacin makarantar. Har ila yau, ya umurci cewa duk wani aikin gyara ya kasance ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi ko ofishin gwamna.
A gefe guda, gwamnan ya duba sabon aikin gyaran Kano Printing Press, wanda aka lalata yayin zanga-zangar #EndBadGovernance a 2024. Ya buƙaci ƴan kwangilar aikin da su tabbata sun bi ƙa’idojin gini da kyau.