Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karyata ikirarin da ake yi na cewa, sun samu sabani da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Abdullahi Baffa Bichi, wanda ya yi sanadiyar tsige shi daga mukaminsa.
Gwamnan ya yi watsi da wannan jita-jitar da cewa, ba ta da tushe ballantana makama a jawabin da ya gabatar a ranar Talata a wurin rantsar da manyan sakatarori 21, masu ba da shawara 15, da kuma shugaban karamar hukuma daya da aka gudanar a gidan gwamnatin da ke Kano.
- Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Ta Ceto Rayuka 417 Da Dukiyoyin Nairori A Shekarar 2023
- Filato: An Kaddamar Da Rundunar Tsaro Ta Musamman
An yi ta yada jita-jita a jihar cewa, an yi sa’in’sa tsakanin Gwamna Yusuf da sakataren gwamnatin jihar wanda hakan ya yi sanadin tsige shi a mukaminsa.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa, Sakataren ya tafi kasar Masar ne domin duba lafiyarsa, wanda hakan ya sa aka nada shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar (HoS), Abdullahi Musa a matsayin mukaddashin Sakataren.
Gwamna Yusuf ya ce, nada HoS na jihar a matsayin mukaddashin SSG ba yana nufin tsige SSG daga mukaminsa ba ne. Ya ce, muhimmancin da ofishin ke da shi, ba zai yiwu a barshi babu kowa ba aciki.
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu SSG yana samun sauki daga rashin lafiyar da ta hana shi aiki na wucin gadi makonnin da suka gabata.
Da yake tabbatar da lafiyar SSG, gwamnan ya sanar da dawowar SSG nan da ‘yan kwanaki kadan domin ci gaba da aikinsa a ofishinsa.