Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Gida-Gida, ya sanar da nadin wasu karin sabbin hadimai a bangarori daban-daban har su 116.
Sabbin wadanda aka nada sun kunshi manyan mataimaka na musamman guda 63, (SSAs), manyan mataimaka (da ba na musamman ba wato ‘SAs’ guda 41, mataimaka na kashin kai (PAs) su 12.
- Gwamnatin Abba Kabir Za Ta Inganta Tsarin Makarantun Tsangayu A Kano – Falaki
- Kotu Ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Filato
Babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Sanusi Bature, ta cikin wata sanarwa da ya rabar wa ‘yan jarida a ranar Juma’a ne ya shelanta hakan.
Bature ya misalta nade-naden na gwamna Yusuf da cewa an yi ne domin cimma burin tafiya da matasa cikin harkokin mulki da kuma janyo jama’a kusa da gwamnati domin tabbatar da cigaba.
“A kokarin da ake yi na shigo da wadanda suka dace kwararru cikin sha’anin gudanar da mulki mai nagarta, gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da nade-naden manyan mataimaka na musamman, manyan mataimaka, da kuma mataimaka na kashin kai, wadanda mafi yawansu matasa ne,” ya shaida.
Ya taya sabbin hadiman murna tare da kira a garesu da su yi aiki tukuri domin taimaka wa gwamnati wajen cimma nasara, kuma su sanya bukatun jama’a farko kafin komai.