Gwamnatin Jihar Kebbi ta raba Naira Biliyan 6.5 ga mutane 65,000 a fadin kananan hukumomi 21 na jihar a karkashin shirin ba da tallafi na ‘Kaura Cares’. Gwamna Nasir Idris ya kaddamar da shirin rabon kudaden a Birnin Kebbi, inda ya bayyana cewa kowane mutum daya zai ci gajiyar tallafin na Naira 100,000, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin jihar ba.
Ya jaddada cewa,shirin ya cika alkawarinsa da ya dauka a lokacin yakin neman zabe kuma ya rubanya wadanda suka fara cin gajiyar shirin har sau hudu. Ya kuma umurci ma’aikatar lafiya ta jihar da ta zakulo masu bukatar daukar nauyin dawainiyarsu wanda jihar za ta dauki nauyin biyan kudaden kulawa da lafiyarsu.
- A Shirye Sin Take Ta Ci Gaba Da Yin Hadin Gwiwa Tare Da Kasashen Afirka Wajen Sa Kaimi Ga Inganta Shirin Rage Talauci
- Shugaban Zanzibar Na Kasar Tanzaniya, Ya Ba Da Lambabin Yabo Ga Tawagar Likitocin Kasar Sin Bisa Taimakon Da Suka Baiwa Zanzibar
Kwamishinan Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsara Tattalin Arziki na jihar Kebbi, Dakta Abba Sani-Kalgo, ya bayyana cewa, Gwamnan ya amince da fitar da zunzurutun kudi har Naira biliyan 6.5 don tallafa wa mutane 65,000 a fadin kananan hukumomi 21 na jihar don amfana da kuma samun gudanar da Sana’o’in dogaro da kaI.
Tun da farko, anata jawabin, Shugabar shirin ‘Kaura-Cares’, Dakta Rukayya Muhammad-Bawa, ta bayyana manufofin shirin da nasarorin da aka samu a wajen taron bikin kaddamar rabon tallafin kudaden a dakin taro na masaukin Shugaban Kasa da ke Birnin Kebbi.