Gwamna Dauda Lawal ya jaddada kudirinsa na kawo karshen yawaitar ayyukan ‘yan ta’adda da da suka addabi jihar Zamfara.
A yau Laraba ne gwamnan jihar Zamfara ya kaddamar da kwamitin amintattu na tsaro na jihar Zamfara mai mambobi 21.
- Matsalar Tsaro: Gwamna Dauda Ya Kaddamar Da ‘Askarawan’ Zamfara
- Gwamnatin Zamfara Za Ta Raba Dabbobi Kyauta Ga Mata
Kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyana haka a takardar da yasanya wa hannu ya raba wa manema labarai a Gusau.
A cewarsa an samar da asusun kula da harkokin tsaro ne domin tara kudade da kuma taimakawa gwamnati don magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a jihar.
Suleiman, ya kara da cewa wadanda za su jagoranci aikin kula da asusun tsaron, sun hada da tsohon Sufeto Janar na ‘Yansanda MD Abubakar, a matsayin shugaba da Dr. Hamza Muhammad a matsayin sakataren gudanarwa.
A lokacin da yake kaddamar da kwamitin bayar da tallafin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa kafa asusun amintatu na tsaro shi ne zai samar da kayan aiki don tallafa wa kokarin gwamnati na magance kalubalen rashin tsaro da ya addabi jihar.