Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya ta amince da aikin babban titin Sakkwato zuwa Badagary kashi na farko.
Gwamnatin tarayya ta kuma amince da gina madatsun ruwa guda 63 domin bunkasa wutar lantarki a kasar nan.
- Ambaliyar Ruwa Ta Raba Hanyar Bauchi Zuwa Kano
- Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Karin Albashi Da Alawus-alawus Ga Ma’aikatan Shari’a
Idris ya bayyana haka ne a wajen bude wani taro na kwanaki biyu na Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya da hukumominta, a ranar Talata a Abuja.
A cewar Idris, akwai bukatar bangarorin yada labarai su fahimci irin kokarin da gwamnati ke yi na samar da romon dimokuradiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp