A ranar Litinin ne Minista Tattali Arziki, Mr Wale Edun, ya karyata rahotattani da ke yawo a kafafen yada labarai cewa, gwamnati ta kara haraji BAT daga kashi7.5 zuwa kashi 10.
A wata sanarwa da ta fito daga ofishin ministan, ya tabbatar da cewa, kudi haraji BAT na nan kamar yadda aka sai na kashi 7.5 a kan kayayyakin da al’umma ke amfani da shi a yau da kullum.
- Sin Ta Kulla Yarjejeniyar Tsarin Kafa Huldar Abota Ta Raya Tattalin Arziki Cikin Hadin Gwiwa Tsakaninta Da Kasashen Afirka 22.
- Matatar Man Dangote: Za Mu Shigo Da Mai Idan Kudin Sufurinsa Ya Fi Sauki Daga Waje -IPMAN
Ya lura da cewa, kashi 7.5 da ake karba a BAT yadda doka ta tanada domin a rika karba a kan kayayyakin da ake amfani da su a na yau da kullum kuma bubu wanda yake da ikon canzawa in ba ta hayar doka ba, hatta gwamnatin tarayya ko kuma wani mai ruwa da tsaki har sai ayi wa dokar da ta samar da harajin kwaskwarima kamar yadda dokar ta bayyana.
Ya kuma kara da cewa, harkar tafiyar da dokar haraji ya tsayu ne a kan abin da ya shafi abu uku su kuma hada da tsari tafi da dokokin haraji da dokokin haraji da kuma tsare-tsare tafiyar da haraji, wanda hakan gwamnati ta tsara kuma babbu wanda zai iya canza wa ba tare da an yi wa dokokin kwaskwarima ba.
“Hankoro mu a halin yanzu shi ne samar da kakkarfar tattalin arziki, rage talauci a tsakanin ‘ya Nijeriya da kuma tabbatar da harkokin kasuwancin suna tafiya yadda ya kamata ta yadda al’umma za su samu riba a harkokin da suke yi.”
A saboda haka muna karyata bayanan da ke fitowa a wasu sashe a gidajen watsa labarai na cewa, za a kara haraji BAT wannan ba gaskiya ba ne, in ma hakan ya taso gwamnatin tarayya na da hanyoyin da za ta sanar da wannan bayanan ta yadda al’umma za su gamsu.
“Al’umma na sane da tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fito da su don ganin an samar da bunkasar tattalin arziki ga ‘yan kasuwanmu musamman ta bayar rage harajin shigo da kayayyaki da kuma cirewa masu shigo da shinkafa haraji da wasu kayan abinci.”
“Muna kara tabbatar da muku cewa, harajin BAT na nan a kan kashi 7.5, haka za mu ci gaba da karba a kayayyakin da ake amfani da su a yau da kullum,” in ji shi.