Kungiyar masu dillanci man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewar za ta shigo da man fetur cikin kasa idan jigilar sufurin shigowa da shi ta fi sauki fiye da jigilar sayen man na Dangote.
Dillalan sun nuna damuwarsu kan yadda ake samu jinkirin sanar da farashin litar mai na matatar mai ta Dangote.
- Kaduna: Ruftawar Hanya Sakamakon Ambaliyar Ruwa Ta Katse Garuruwa Biyar A LereÂ
- Kotu Ta Bada Belin Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Kan Naira Milyan 10 Kowanensu
Shugaban IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce a halin yanzu ana sayen litar mai a kalla kan naira 1,120. Ya kara da cewa matukar farashin matatar mai na Dangote ta zarce wannan adadin, to ‘yan kasuwa za su ci gaba da shigo da mai daga waje zuwa cikin kasar nan.
“Idan farashin shigo da mai ya fi na Dangote sauki, za mu ci gaba da shigo da shi daga waje, amma idan na shi ya fi na waje sauki, za mu ga yadda za mu yi mu saya.
“Abu ne a kasuwa, ko a ina muka ga mai da sauki da inganci tabbas nan za mu sa kai, nan za mu je mu sayo. Ba mu san farashin litar mai na Dangote ba har yanzu, amma muna tattaunawa da abokan kasuwancinmu na waje.
“Idan aka bai wa kowa damar kawo kayansa, za a samu gasa ta hanyar haka za a samu saukin farashin. Masu shigowa da shi za su yi kokarin saukakawa, nan ma na cikin gida za su yi kokarin sayarwa kasa da yadda za a so saya.”
Rahotonnin sun ce shugaban runkunan kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya taba shaida cewar suna jiran NNPCL ne domin tsaida farashi.
Ya ce akwai yarjejeniyar farashi da aka samu daga wajen gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu. Ya ce da zarar aka kammala cimma matsaya, matatarsa za ta fara shigo da kayanta kasuwa ta hannun kamfanin NNLPCL.
Shi kuma Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye, ya ce za su yi mai daga wajen matatar nai ta Dangote ne kawai idan farashinsa ya yi sauki kasa da na kasuwannin duniya.