Gwamnatin tarayya ta shelanta cewa a yanzu, don tunkarar noma a bana, ta tanadi ingantaccen Irin noma tan 89,512.10
Minitan aikin noma da raya karkara Dakta Mohammad Mahmood Abubakar ya sanar da hakan a lokacin kaddamar tsarin samar da Irin noma na shekarar 2022, da aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja.
Dakta Mohammad ya bayyana cewa, wannan kundin tsarin samar da Irin, ya nuna irin namijin kokarin da hukumar samar da ingantane Iri ta kasa NASC.
Ministan ya kara da cewa, kokarin ya kuma hada da na sauran masu ruwa da tsaki, musaman domin a tabbatar da manoman kasar sun samu ingantaccen Irin da kuma sauran kayan aikin noma, musamman na zamani.
Dakta Mohammad ya ce, hakan zai taimaka wa manoman kasar nan wajen noma afnain gona mai yawa da zai wadaci ‘yan Nijeriya.
“Kokarin ya kuma hada da na sauran masu ruwa da tsaki, musaman domin a tabbatar da manoman kasar sun samu ingantaccen Irin da kuma sauran kayan aikin noma, musamman na zamani.”
A cewar Dakta Mohammad,“Ina son in kara nanata cewa, sabunta wannan tsarin da aka yi, zai kawara da kalubalen da aka fuskanta a tsarin da aka yin a kasa na samar da Irin a shekarar 2015.”
Dakta Mohammad ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da aka samu na gabatar da tsarin samar da takin, musamman yadda aka samar da mai inganci.
Ministan ya kara da cewa, tsarin zai kuma taimaka wajen magance samar da gurbataccen Irin da dabi’ar ‘yan na kama.
Dakta Mohammad ya sanar da cewa, har ila yau, tsarin zai taimaka wajen yin gwajin Irin a dakin yin gwaje-gwajen da kuma kara bai wa, musamman mata da matasa da ke da sha’war shiga fannin yin noma a kasar nan.
“Wannan tsarin zai taimaka wajen yin gwajin Irin a dakin yin gwaje-gwajen da kuma kara bai wa, musamman mata da matasa da ke da sha’war shiga fannin yin noma a kasar nan.”