ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da Sarakuna Da Gundumomi

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
6 months ago
Gwamna Bala

A wani mataki na yunkurin cika alkawuran da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya dauka a lokacin yakin neman zaben da ya gabata da kuma kiranye-kiranyen da aka samu daga sassan jihar, gwamantin jihar ta yi kira ga al’ummomin da suke da ra’ayi kuma suke so, da su mika bukatar neman kirkirar sabbin masarautun gargajiya, sarakuna ko gundumomi.

Mashawarcin gwamnan Jihar Bauchi kan hulda da ‘yan jarida, Kwamared Mukhtar Gidado shi ne ya sanar da wannan matakin ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce, za a bude damar amsar bukatar ne daga ranar Talata 10 ga watan Yuni zuwa 8 ga watan Yulin 2025.

  • Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya
  • Cikakken Jerin Sunaye: Tinubu Ya Karrama ‘Yan Nijeriya 102 Don Bukin Ranar Dimokuradiyya Ta 2025

Dukkanin bukatar nema za a aike ne zuwa ofishin babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da kula da harkokin masarautun gargajiya da ke cikin Abubakar Umar Secretariat ta Bauchi.

ADVERTISEMENT

Gidado ya kara da cewa kowani bukatar nuna sha’awar nema dole ne a fitar da shi har kwafi guda 15.

Gwamnatin jihar ya kuma ce dole ne kowani bukata ya zama an samar da muhimmin shafin farko da zai kunshi cikakken sunan masarauta, sarki ko gundumar da ake nema, tare kuma da bayyana balo-balo kan sunan masarauta ko gundumar da karamar hukumar da ake neman sabon masarautar ko sarki ya fito daga ciki.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

A cewarsa, dukkanin takardar neman kirkirar sabon masarauta ko sarki ko gunduma dole ne a aike zuwa addireshin gwamnan jihar ta hannun babbar sakatariyar ma’aikatar kananan hukumomi da kula da masarautu na jihar.

Kazalika, ya ce dole ne masu nema su gabatar da takaitaccen tarihin al’ummar da suke nema wa masarauta ko sarki ko gudunmawa tare da tarihin masarautar ko sarki ko gundumar da ke yankin da suke neman fita daga ciki.

Sanarwar ta kuma nemi a sanya dukkanin wani muhimmin bayanin da aka san zai iya taimakawa wajen la’akari da bukatar masu nema.

Har ila yau, sanarwar ta ce dole ne a takardar neman a samu sahihin sanya hannun hakimi, sarakunam kauye, da shugabannin al’umma tare da tabbacin wannan neman ta fito ne daga al’ummar wannan yankin da ake nema mata masarauta ko sarki ko gunduma.

Sanarwar ta kara da cewa duk al’ummomin da ke son kirkirar sabbin masarautu, sarakuna, ko gundumomi su na da dama kuma su na da ‘yancin gabatar da bukatar neman.

Gidado ya jaddada cewa shirin na daya daga cikin kudirin gwamnati na bunkasa gudanar da harkokin kananan hukumomi, da kiyaye al’adu, da karfafa cibiyoyin gargajiya a matsayin muhimman ginshikan zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba masu ma’ana.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Matsin Rayuwa: ‘Yan Nijeriya Sun Rage Zuwa Kasashen Waje

Matsin Rayuwa: 'Yan Nijeriya Sun Rage Zuwa Kasashen Waje

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.