Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN), ya bayyana cewa gwamnatin Buhari za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaron kasar nan kafin karewar wa’adinsa.
Malami ya bayyana hakan ne a cikin sakon murnar sallar ga al’ummar Musulmin kasa da na Jihar Kebbi kan murnar zagayowar sallah.
- Jaridar Daily Trust Ba Ta Yi Mana Adalci Ba- Fadar Shugaban Kasa
- Mataimaki: Gwamnonin APC Na Alfahari Da Zabin Tinubu – Bagudu
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarar da sakataren yada labaransa, Ibrahim Abubakar Dakingari, na kungiyar Khadimmiya da ya sanyawa hannu aka kuma rabawa manema labarai a Brinin Kebbi.
Minista ya ce”Bikin sallah na tunatar da musulmi da su kasance masu biyayya da zuciya daya ga umarni da dokokin Allah madaukakin Sarki kamar yadda Annabi Ibrahim, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi.”
“Gudanar da wannan gagarumin biki, ya kamata mu yi tunani a kan darussa na asali na hakuri, sadaukarwa da mika wuya ga yardar Allah da Annabi Ibrahim ya nuna a lokacin da Allah ya umarce shi da ya yanka dansa tilo (Isma’ila), ta hanyar sadaukar da kanmu ga kara riko da dokokin Ubangiji da kuma nuna hakikanin ruhin Musulunci a cikin dukkan ayyukanmu.
“Yayin da mu ke bikin babbar sallah, dole ne mu yi la’akari da duk abubuwan da ke faruwa a kasarmu, domin mu yi amfani da lokacin yin addu’a don Allah ya kawo mana dauki ga matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke addabar kasar nan wanda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke ciki, inji shi”.
Haka kuma ministan ya kuma yi kira ga ’yan uwanmu maza da mata a kasa mai tsarki da suke gudanar da aikin hajjin bana da su yi ta addu’a domin neman fansa.
“Ina kara sake tabbatar muku cewa gwamnatin Buhari za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaron kasar nan.
“Ina addu’ar Allah ya karbi addu’o’inmu na ganin an samu dawamammen zaman lafiya a jihar Kebbi da kasa baki daya tare da samar da zaman lafiya a siyasance,” in ji Malami.