Daya daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, mai suna Hassan Usman da ya kubuta da yammacin yau Litinin, ya ce gwamnati ce ta harzuka ‘yan ta’addan suka fara gana musu azaba.
Usman ya kubuta tare da wasu mutane biyu; mace daya da namiji daya.
- ‘Yan Ta’adda Sun Kai Wa Sojoji Hari A Abuja
- Jami’an Tsaro Sun Kashe Mahara 2 A Anambra, Sun Kwato MakamaiÂ
A tattaunawarsa da BBC Hausa, ya bayyana irin halin da ya tsinci kansa tare sa sauran wadanda ‘yan ta’addan suka sace a lokacin harin jirgin kasan.
“Da farko a waje muke kwana a kasan bishiya, amma da aka fara ruwan sama sun yi mana rumfa da shimfidu da muke kwana a kai.”
Ta fuskar abinci kuwa, ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun yi kokari iyakarsu wajen ganin sun ba su cima mai kyau.
“Eh to abinci alhamdulilah suna iya kokarinsu gaskiya, suna ba mu abinci daidai karfinsu a wani lokaci ma har yanka suke mana na shanu da awakai.
“Akalla ko jiya (Lahadi) sun yanka mana sa mun ci alhamdulilah,” in ji shi.
Sai dai kuma ya ce gwamnatin tarayya ta fusata ‘yan ta’addan wanda hakan ya sa suka fara dukansu, kuma sun shirya gana musu azaba iri-iri.
“Eh to tun da muka je, gwamnati ce ta harzuka su har suka fara daukar matakai na duka kamar yadda kuka gani a bidiyon da aka sani, mun sha duka matukar duka.
“Kuma wannan ma somin tabi ne saboda har yanzu ‘yan uwana ina jimamin cikin yanayin da zasu sake shiga idan ba a kawo musu dauki ba, shi yasa wannan bidiyon ya fito.
“Shi yasa muka yi kira ga wasu kasashen tun da muna ganin mu gwamnatinmu ta Nijeriya ta gaza har muka zauna wajen wata hudu,” in ji shi.
A karshen mako ne dai ‘yan ta’addan suka saki wani sabon bidiyo suna dukan fasinjojin da suka yi garkuwa da su.
Hakan ya harzuka ‘yan Nijeriya da dama, inda kowa ke ganin gwamnatin tarayya gaza samar da tsaron da take ta ikirari.