Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana cewa nan bada daɗewa ba gwamnatin jihar za ta magance rikicin manoma da makiyaya daya daɗe yana haifar da babbar barazanar tsaro a ƙasar nan.
Njoɗi ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin tawagar aiwatar da Shirin Zamanantarwa da Bunƙasa Kiwo wato (L-PRES) yayin wata ziyara da suka kai masa a gidan gwamnati.
- ‘Muna Cikin Fargabar Yiwuwar Ambaliyar Ruwa A Daminar Bana’
- Sharhi: Sin Da Amurka Ba Su Bukatar Zama Abokan Gabar Juna
Ya ce shirin wanda Bankin Duniya ke ɗaukar nauyi, an samar da shi ne sakamakon siyasantar da shirin bunƙasa kiwo na gwamnatin tarayya, wanda aka tsara da nufin zamanantar da sana’ar, saɓanin yadda ake yinta a fili sakaka, lamarin da ke haddasa rikici tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan.
Sakataren gwamnatin ya ce duba da ɗimbin damammakin da Jihar Gombe ke da su a harkar noma da kiwo, da kuma babban gandun kiwon da ta ke da shi na Wawa-Zange, gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ga wajibcin lalubo sabbin hanyoyin cin gajiyar arziƙin da Allah ya huwacewa jihar don amfanin al’ummarta.
Da yake yabawa tawagar bisa jajircewarta na ganin an inganta kiwon a ƙarƙashin sabon shirin da jihar ta shiga, sakataren ya koka da cewa Nijeriya ba ta cin moriyar arziƙin dabbobinta yadda ya kamata.
“Ba ma morar arziƙin dabbobin da muke da su yadda ya kamata. Babu wani abu da za a ce ya zama shara a yau, ƙasashen da suka ci gaba suna amfani da komai na dabbobi.”
“Akwai wasu hanyoyin da za mu ƙara amfana da waɗannan dabbobi ban da madara da nama; me muke yi da jinin da ke zuba a banza? Ana iya iya amfani da shi wajen yin abincin wassu dabbobin, abin da ƙasashen da suka ci gaba suke yi ke nan. Ƙashin fa me muke yi da shi?, Mai laushin kawai muke ci, mu zubar da mai taurin, za a iya amfani da shi ta wasu hanyoyin. Ina hanji da sauran kayan ciki? Wasu daga ciki kawai ake amfani da su a watsar da sauran, za a iya amfani da su a matsayin taki da sauran fa’idodi” in ji shi.
Ya ce baya ga alfanun shirin ta fuskar tattalin arzikin, L-PRES zai taimaka wajen samar da dauwamammiyar mafita ga matsalar tsaron da ta samo asali daga rikicin manoma da makiyaya a kasar nan.
Da yake yabawa tawagar aiwatar da shirin bisa jajircewarta da ya kai ta ga samun lamunin na Bankin Duniya don gudanar da shirin, Njoɗi ya buƙaci shugabannin shirin su yi watsi da duk wani nau’in alfarma ko sanayya tare da yin waje da duk wanda bai shirya bada gudummawar da za ta kai ga samun nasarar shirin ba.
Njoɗi ya yi gargaɗin cewa “Yanzu za a iya cewa kuna yi wa Bankin Duniya aiki ne, kuma shi bai san wata abota, zumunta ko dangantaka ba, abin da yake so kawai shi ne ku yi aiki a yi nasara. Don haka kar ku bamu kunya. Mun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da bankin, yanzu wannan shiri ya zama namu. Idan wani ya ƙi yin abin da ya kamata, ku shaida mana za mu kore shi”.
Ya buƙaci shugabannin shirin na L-PRES kar su yi ƙasa a gwiwa, su jajirce wajen ganin tattalin arzikin Jihar Gombe da na manoma da makiyaya ya bunƙasa.
Ya kuma bada tabbacin gwamnatin jihar na ci gaba da bai wa shirin haɗin kai da goyon baya don samun nasararsa.
Tun farko a jawabinsa, shugaban tawagar kuma kodinetan shirin Dokta Usman Bello Abubakar, ya ce shirin an samar da shi ne da nufin faɗaɗa harkokin noma a jihar, musamman a ɓangaren kiwo.
Ya ƙara da cewa shirin zai kuma magance rikicin manoma da makiyaya da ke ci gaba da salwantar da rayuka da dukiyoyi a jihar dama Nijeriya.
Ya ce kiwo sana’a ce mai riba wadda ke inganta tattalin arzikin ɗaiɗaikun jama’a, da na jiha da ma ƙasa baki ɗaya.
Da yake bayyana cewa Jihar Gombe ce ta uku a Nijeriya wajen cika sharuɗan samun lamunin Bankin Duniya, kodinetan ya yabawa gwamnan jihar, da kuma goyon baya da kyakkywan jagorancin da sakataren gwamnatin jihar ke bai wa tawagar.
Tawagar ta taya Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya murnar sake zaɓensa, da kuma Farfesa Njoɗi bisa sake naɗin da aka yi masa a matsayin sakataren gwamnatin jihar, inda ya bayyana Njoɗi a matsayin shugaba mai sauƙin kai a mu’amala kuma jagora abun koyi.