Gwamnatin Jigawa ta amince da fitar da Naira biliyan 1 don samar da ayyukan kiwon lafiya kyauta ga marasa karfi a jihar.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu, Alhaji Sagir Musa ne ya bayyana hakan jim kadan bayan taron majalisar zartarwa ta jihar a Dutse.
- Wuraren Shakatawa Na Beijing Sun Gabatar Da Shagulgulan Al’adu 109 Albarkacin Hutun Bikin Bazara
- Kamfanin OSP Na Kasar Saudiyya Zai Hadin Guiwa Da Nijeriya Kan Shirin Samar Da LPG
Kwamishinan ya ce, amincewar ta biyo bayan wata takarda da ma’aikatar lafiya ta gabatar inda tace, za a yi amfani da Naira biliyan 1 daga asusun ba da lamuni na jihar domin gudanar da shirin kiwon lafiya kyauta.
“Asusun na da nufin samar da ayyukan kiwon lafiya kyauta ga marasa karfi na tsawon watanni 12,” in ji Musa.
Ya ce wannan matakin na daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na cimma nasarar Kariyar Lafiya ta Duniya.
A cewarsa, jimillar mutane 143,500, daga sassan siyasa 287 na jihar ne ake sa ran za su ci gajiyar shirin kiwon lafiyar kyauta.