Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanar da bayar da guraben tallafin karatu ga fiye da ɗalibai 200 da suka halarci gasar karatun Alƙur’ani ta jihar karo na 40. Wannan mataki, a cewar gwamnan, na nufin karfafa hadin ilimin addini da na zamani domin gina kyakkyawar al’umma.
A lokacin da yake jawabi a wajen rufe gasar karatun Alƙur’ani da aka gudanar a ɗakin taro na Sir Ahmadu Bello, Dutse, Gwamna Namadi ya ce dukkan mahalarta za su samu tallafi a fannonin da suka zaɓa, ciki har da ilimin Alƙur’ani da Hadisi, da Fasaha, da Injiniyanci, da Likitanci da Kimiyya. Ya jaddada cewa gwamnati na da niyyar ci gaba da tallafa wa ɗalibai masu hazaƙa don tabbatar da cewa kowane ɗan Jigawa ya samu damar koyo da ci gaba da ilimi cikin aminci.
- Za mu Inganta Fannin Karatun Alkur’ani – Gwamnan Jigawa
- Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnati ta tanadi kasafi na musamman don inganta koyar da Alƙur’ani da ilimin addini, tare da sauya tsarin almajiranci zuwa tsari mai daidaito da ilimin zamani. A cewarsa, wannan tsarin zai taimaka wajen gyaran halaye da gina tarbiyyar al’umma, domin waɗanda suka samu ilimin addini na gaskiya sukan zama ginshiƙin gaskiya da kyawawan halaye a cikin al’umma.
A cewar Namadi, hukumar Tsangaya da aka kafa kwanan nan za ta taka muhimmiyar rawa wajen haɗa ilimin Alƙur’ani da na boko ta hanyar tsare-tsare na zamani, don tabbatar da cewa yara da matasa suna samun ilimi mai amfani ga addini da rayuwa gaba ɗaya.
Sakataren Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar Jigawa, Dr. Mubarak Abdulwahab Hassan, ya yaba wa Gwamna Namadi bisa wannan gagarumin mataki, yana mai cewa wannan tallafi zai taimaka wajen haɓaka karatun Alƙur’ani, da kuma inganta sha’awar matasa wajen neman ilimi na addini da na zamani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp