• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Jihar Enugu Ta Haramta Hakar Ma’adinai Ta Haramtacciyar Hanya

by Muhammad
2 years ago
Enugu

Gwamnatin jihar Enugu ta sanar da hana hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Chidiebere Onyia, ne ya sanar da dakatarwar a ranar Juma’a a Enugu, yayin da yake kaddamar da kwamitin da zai duba ayyukan hakar ma’adanai a jihar.

  • Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutum 5 A Enugu
  • ‘Yan Awaren Biyafara 30 Sun Shiga Hannun ‘Yansanda A Jihar Enugu

Onyia ya yi gargadi tare hukunta duk wani mai hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ko wanda ya saba wa umarnin gwamnati.

Ya ce, “Gwamnati ta lura cewa yana da matukar amfani ga jama’a su kare kansu daga duk wani hadari ko gurbacewar yanayi, tare da tabbatar da daidaiton hakkokin fa’idojin da za a iya samu daga duk wani albarkatun ma’adinai ga mutanen Enugu.”

A cewarsa, haramcin ya biyo bayan umarnin Gwamna Peter Mbah kan rahoton gano albarkatun ma’adinai a wasu yankuna da kuma hakar albarkatun ba tare da izinin gwamnati ba.

LABARAI MASU NASABA

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

An ruwaito cewa kwamitin na karkashin jagorancin kwamishinan muhalli, Farfesa Sam Ugwu.

Mambobin sun hada da babban lauya kuma kwamishinan shari’a, Dr Kingsley Udeh, mai bawa gwamna shawara na musamman kan makamashi da albarkatu, Kingsley Nnaji, mai bawa gwamna shawara na musamman akan harkokin shari’a, Osinachi Nnajieze, da babban jami’in tsaro na gidan gwamnati, Mr Alex. Akinlalu.

Sauran mambobin sun hada da babban mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin tsaro, Onyeator Vincent, babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai, Dan Nwomeh, babban mataimaki na musamman ga gwamna kan hulda da kasashen waje, Uche Chukwu, da kuma mai taimakawa gwamna na musamman kan kudaden shiga, Sandra George.

Sakataren gwamnatin ya ce ayyukan kwamitin sun hada da gano wuraren hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, dakatar da duk wani aikin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, duba duk wasu takardun tantance muhalli na duk kamfanonin hakar ma’adanai da kuma sake tantancewa da sake tabbatar da duk kamfanonin hakar ma’adanai a jihar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan
Manyan Labarai

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026
Manyan Labarai

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba
Ilimi

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Next Post
Dawowa Hutu: Iyaye Sun Koka Kan Karin Kudin Makaranta A Yanayin Kuncin Rayuwa

Dawowa Hutu: Iyaye Sun Koka Kan Karin Kudin Makaranta A Yanayin Kuncin Rayuwa

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025
Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

October 13, 2025
NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

October 13, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

October 13, 2025
Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin

October 13, 2025
Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.