• English
  • Business News
Monday, September 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Jihar Gombe Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Domin Gina Mayankar Dabbobi

by Abubakar Abba
4 months ago
in Noma Da Kiwo
0
Gwamnonin Arewa Na Kokarin Farfado Da Hadin Kan Yankin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin Jihar Gombe, ta kulla wata yarjejeniya da kamfanin ‘Label Nigeria’, domin gina katafariyar mayankar dabbobi ta zamani a jihar, wacce ake sa ran za ta lashe kudi har kimanin Naira biliyan uku.

Wanan dai, na daya gaba bangare na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi a fadin jihar ta Gwambe.

  • Darajar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso Shida Bisa Dari A Afirilu
  • Tsaro Ya Inganta A Zamfara, In Ji Gwamna Lawal Yayin Tattakin Zaman Lafiya Na Tarihi A Jihar

Kazalika, aikin na daga cikin bangaren shirin inganta kiwon dabbobi tare da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi wato (L-PRES).

Babban Bankin duniya ne ke tallafa wa wannan shiri, da manufar kara kyautata harkokin kiwon dabbobi tare kuma da sarrafa nama cikin tsafta a fadin jihar.

An dai kulla wannan yarjejeniya ce tare da kamfanin ‘Lubel Nigeria’ da wa’adin kammalawa na wata tara, ma’ana zuwa watan Fabrairun shekarar 2025.

Labarai Masu Nasaba

Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

A jawabinsa a wajen rabbata hannun yarjejeniyar, jami’in shirin na jihar ta Gwambe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya danganta wannan aiki a matsayin wani babban ci gaba a jihar.

Ya kara da cewa, aikin ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, akwai kuma batun zuba hannun jari ga ci gaban kiwon su kansu dabbobin.

A cewarsa, za su tabbatar da aiki da ka’idojin duniya wajen tsafta, yanka da kuma sarrafa nama.

Jami’in ya kuma yaba wa gwamnan na Jihar Gombe, Inuwa Yahaya bisa hangen nesansa na kokarin kyautata samar da kayan more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya.

Shi kuwa a nasa jawabin, shugaban gudanarwa na kamfanin Arch. Yunusa Yakubu, ya yi alkawarin kammala aikin cikin inganci, sannan kuma a kan lokaci.

Ya kuma bayar da tabbacin, cika dukkanin sharuddan da suka wajaba, domin tabbatar da nasarar aikin.

A cewar Yunusa, da zarar an kammala aikin; ana sa ran zai kawo sauyi mai amfani ga harkar sarrafa nama a Gombe tar kuma da rage hadarin rashin tsaftar da ke tattare da hanyoyin gargajiya da samar da damammaki a kiwon na dabbobi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Gombe
ShareTweetSendShare
Previous Post

Nau’ikan Amfanin Gona Da Ke Saurin Girma Cikin ‘Yan Watanni

Next Post

Jami’ar Jos Ta Samu Lambobin Zinare 14 A Gasar NUSSA, Yayin Da FUT Daura Ta Lashe Kofin Kwallon Kafa

Related

Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

1 week ago
Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON
Noma Da Kiwo

Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

1 week ago
Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

3 weeks ago
Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025
Noma Da Kiwo

Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

3 weeks ago
Kwararre Ya Ja Hankali Kan Sayar Da Takin Zamani Da Ba A Tantace Shi Ba
Noma Da Kiwo

Kwararre Ya Ja Hankali Kan Sayar Da Takin Zamani Da Ba A Tantace Shi Ba

1 month ago
Manoman Doya 100 A Jihar Nasarawa Suka Amfana Da Horon Cibiyar NEPC
Noma Da Kiwo

Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu

1 month ago
Next Post
Jami’ar Jos Ta Samu Lambobin Zinare 14 A Gasar NUSSA, Yayin Da FUT Daura Ta Lashe Kofin Kwallon Kafa

Jami’ar Jos Ta Samu Lambobin Zinare 14 A Gasar NUSSA, Yayin Da FUT Daura Ta Lashe Kofin Kwallon Kafa

LABARAI MASU NASABA

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja

September 15, 2025
Arewa Ba Zata Ƙarɓi Mulki A 2027 Ba, Gwamna  Bago

Arewa Ba Zata Ƙarɓi Mulki A 2027 Ba, Gwamna  Bago

September 15, 2025
KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

September 15, 2025
Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

September 15, 2025
Barcelona Ta FarfaÉ—o Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff

Barcelona Ta FarfaÉ—o Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff

September 15, 2025
Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)

Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)

September 14, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Madrid

Sin Da Amurka Sun Fara Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Madrid

September 14, 2025
An Gano Gawar Yarinyar da Ruwan Sama Ya Tafi Da ita A Zariya

An Gano Gawar Yarinyar da Ruwan Sama Ya Tafi Da ita A Zariya

September 14, 2025
Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana

Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana

September 14, 2025
Za A Kaddamar Da Fim Mai Taken 731 A Sassan Duniya

Za A Kaddamar Da Fim Mai Taken 731 A Sassan Duniya

September 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.