Gwamnatin Jihar Taraba, ta bayyana kudurinta na yi wa kasuwannin sayar da dabbobi guda tara na jihar garanbawul tare da kuma gyara mayankar dabbobi biyar da ke jihar.
Hakan na daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na samar da dabaru, domin cin gajiyar da ke fannin.
- An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba
- Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi
Kwamishinan Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci na jihar, Farfesa Nicholas Oliber Namessan, ya sanar da hakan ne inda ya ce; aikin zai taimaka wajen inganta tsafta da kuma kula da lafiyar dabbobin.
Ya kara da cewa, Allah ya albarkaci Jihar Taraba da dimbin dabbobi, wanda kuma gwamnatin jihar za ta yi dukkan mai yiwuwa, wajen samar da kayan aiki tare da kara bunkasa fannin kiwo na jihar.
Kazalika, ya sanar da cewa; gwamnatin za kuma ta tabbatar da ta kara bunkasa kasuwancin fannin, musamman domin wadanda suke a fannin su kara samun kudaden shiga tare da kuma kara samar wa da gwamnatin kudaden shiga.
Nicholas, ya sanar da hakan ne, ta bakin wakilinsa Daraktan Kula da Harkokin Dabbobi da ke Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci na jihar, Daudu A. Mbaamo
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, har yanzu fannin aikin noma, da shi jihar ta dogara a kai, musamman duba da cewa; fannin na bayar da gudumawa wajen kara samar da wadataccen abinci a jihar da kuma kara samar da ayyukan yi.
Haka zalika, ya koka da cewa; duk a irin wadannan dimbin albarkatun noma da kuma yawan dabbobin da Allah ya wadaci jihar da su, amma har yanzu jihar na ci gaba da fuskantar kalubalen karancin kasuwannin sayar da dabbobin.
Kwamishinan ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta himmatu, wajen kara habaka fannin kiwon jihar, wanda tuni ta tuntubi ‘yan kwangilar da za su yi aikin gyaran mayankar tare kuma da samar da kayan aiki na bunkasa kiwon dabbobi a jihar.
“Fannin kiwon dabbobi, na daya daga cikin fannonin da ke habaka tattalin arzikin Jihar Taraba da samar da wadataccen abinci da samar da ayyukan yi da kuma kara samar da kudaden shiga, “ a cewar Kwamishinan.
“Hakan ne ya sanya gwamnatin jihar, za ta samar da kayan aiki a fannin kiwon jihar, musamman domin cin gajiyar da ake da ita, daga fannin wanda kuma hakan zai amfanar da al’ummar jihar, in ji Nicholas.
A jawabinsa tun da farko, jami’in aikin tallafa wa kiwon dabbobi na L-PRES Hananiah Albert, ya jaddda kudurin aikin wajen ganin an cimma burin da aka sanya a gaba.
“Za mu tabbatar da mun bi dukkannin ka’idojin da suka dace, wajen wanzar da wannan aiki, domin cimma nasarar da aka sanya a gaba, “in ji Albert.
Ya kara da cewa, manufar aikin ita ce; domin mayar da hankali wajen habaka fannin hada-hadar kasuwancin kiwon na dabbobi da kuma kara bunkasa tattalin arzikin fannin tare da tabbatar da kula da lafiyar dabbobi a fadin jihar.
A cewarsa, a yanzu haka; akwai sama da kasuwannin sayar da dabbobi goma da ake gudanar da hada-hadar a kowane mako, wanda kuma suke da bukatar a yi musu garanbawu domin samar da saukin gudanar da yin hada-hada a cikinsu tare da kuma samar da tsaro.