Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da bayar da hutun wata 6 ga dukkan ma’aikatan gwamnati mata da suka haihu, domin ƙarfafa shayar da jarirai nono cikin watanni na farkon rayuwarsu.
Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Balarabe, ce ta bayyana hakan yayin wani taron bikin Ma-kon Shayar Da Jarirai Nonon Uwa ta Duniya na 2025 da aka gudanar a Kaduna.
- Uwargidar Gwamnan Katsina Ta Nemi A Taimaka Wa Mata Wajen Yaƙi Da Ciwon Nono Da Na Mahaifa
- SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai
Taron ya samu halartar ƙungiyoyin raya ci gaban al’umma, wakilan ƙungiyoyin fararen hula, da kuma jami’an asusun kula da raya na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF).
Ta bayyana cewa shayar da jarirai nono kaɗai yana rage yawan kamuwa da cututtukan yara, yana rage kashe kuɗaɗen kula da lafiya, tare da inganta ƙwaƙwalwa da ƙwarewar tunani a wajen jarirai.
A nata jawabin, Kwamishinar Lafiya ta Jihar Kaduna, Umma Ahmed, ta bayyana cewa ma’aikatar ta buɗe ɗakin kula da jarirai a shalkwatanta domin tallafa wa matan da ke shayar da jarirai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp