Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya ta Jihar Kaduna (KADSUBEB), ta ce ta sallami malaman makaranta 2,357 sakamakon faduwa jarabawar da ta sake shirya musu a kwananakin baya.
Kakakin hukumar, Hauwa Mohammed ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi.
- NiMet Ta Yi Hasashen Samun Hadari Da Tsawa Na Kwanaki 3 Daga Ranar Litinin
- Kwankwaso Ba Zai Yi Wa Peter Obi Takarar Mataimaki Ba — NNPP
Ta ce sun shirya jarabawar ce ga malamai sama da 30,000 a watan Disambar 2021.
A cewarta daga malaman firamare 2,192, ciki har da Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT), Misis Audu Amba, aka sallama daga aiki saboda kin zana jarabawar.
Ta ce akwai wasu malamai 165 daga cikin 27,662 da suka zana jarabawar da su kuma aka kore su saboda rashin kokari.
“Mun gano cewa ba mu da bukatar dukkan malaman da suka samu kasa da kaso 40 cikin 100 na maki a jawabawar, saboda haka mun sallame su daga aiki.
“Malaman kuwa da suka samu kaso 75 cikin 100 su ne muka tantance a matsayin kwararrun malamai da suka cancanta su ci gaba da koyarwa kuma za su fara zuwa kwasa-kwasai kan shugabanci da gudanarwar makarantu,” inji ta.
Da yake mayar da martani kan batun, Shugaban NUT na Jihar, Ibrahim Dalhatu, ya yi watsi da jarawabar da ma korar da aka masa, inda ya bayyana su a matsayin wadanda aka yi ba bisa ka’ida ba.
Sai dai ya ce tuni kungiyarsu ta samu umarnin kotu da ya hana gwamnati shirya jarabawar, amma duk da haka ta yi kunnen uwar shegu da umarnin.
Shi ma da yake maida martani, shugaban NUT na kasa, ya ce suna sane da lamarin, kuma za su zauna ranar Laraba don tattaunawa a kan batun.
A shekarar 2018, gwamnatin jihar ta kori malamai 21,780 da suka fadi jarabawar, sannan ta maye gurbinsu da wasu 25,000.
Har wa yau, a watan Disamban 2021 ta sake sallamar wasu malaman guda 233 saboda amfani da takardun bogi.