Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya a yankin Nasarawa da Trikania.
Wannan na cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce a yanzu dokar za ta fara aiki ne daga karfe 7 na dare zuwa karfe 7 na safe, daga ranar Laraba.
- Hukumar NAFDAC Ta Bankado Magunguna Marasa Rajista Na Naira Miliyan 15 A Abuja
- Shettima Ya Yi Alkawarin Kawo Karshe Kwace Da Markade Babura A Abuja
Aruwan ya ci gaba da bayyana cewa, wannan ya biyo bayan bayanan tantance al’amura daga hukumomin tsaro.
“Daga ranar Laraba 5 ga watan Afrilu, 2023, dokar za ta fara aiki daga karfe 7 na dare zuwa 7 na safe.”
Ya kuma bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su ci gaba da gudanar da ayyukansu a tsakanin wannan lokaci.
Ya kuma ya shawarce su da su bi dokar hana fita da kuma gudanar da aikinsu cikin tsari yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankunan da lamarin ya shafa.