• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kaduna Za Ta Horas Da Ɗalibai 32,000 Sana’oin Hannu A Duk Shekara – Maiyaki

by Shehu Yahaya and Sulaiman
1 month ago
Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta sanar da shirinta na horas da kuma yaye dalibai 32,000 a duk shekara ta hannun Cibiyar Horas da Sana’o’i da Ƙwarewa da aka kafa kwanan nan.

Cibiyar wadda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar a watan Yuni na da rassan da aka tsara su da kyau a Rigachikun, Soba da Samarun Kataf. Rassan cibiyar sun samu kayan aiki na zamani domin samar da horo na dindindin, wanda zai ba da kwarewa ta zahiri da ta zamani da kuma ta duniya.

  • Yaushe Za Ta Kare Wa Haaland?
  • Uba Sani Ya Jagoranci Yunƙurin Ƙara Yawan Rajistar Masu Zaɓe a Jihar Kaduna

Dalibai na iya yin rajista a cikin kowanne daga cikin fannoni 14 na sana’o’in da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa (NBTE) ta amince da su, waɗanda suka haɗa da: Fenti da Kwalliya (POP/, Gini da Sanya Tiles da Bututun Ruwa (Plumbing), Kere-kere da Gyaran Katako Walda da Kera Karfe daq Sanya Wutar Lantarki da Kera Aluminium da Firiji da A/C da kuma Sanya Hasken Rana sai kuma Gyaran Kwamfuta , Girki da Kulawa da Baƙi da Ƙira da Dinkin Kaya.

LABARAI MASU NASABA

Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5

Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta 

Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki.

Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun ƙwararrun ma’aikata a bangarorin gine-gine, makamashi, fasahar zamani (ICT), kula da baƙi, da harkokin ƙirƙira. Muna da yakinin cewa waɗanda suka kammala karatu a wannan Cibiyar ba kawai za su samu ayyukan yi ba ne, har ma za su zama masu dogaro da kai kuma su samar da dama ga wasu.”

Shima Shugaban Cibiyar, Malam Husaini Haruna Muhammad, ya jaddada muhimmancin da horon ke da shi wajen dacewa da bukatun kasuwanni da wuraren aiki: “Abin da muke mayar da hankali a kai shi ne samar da daliban da suka kammala karatu waɗanda suke da shirye-shiryen fuskantar kasuwa da wuraren aiki. Kashi 80% na horonmu yana kasancewa ne na aikace-aikace, wanda ke ba wa ɗalibai damar samun ƙwarewar rayuwa ta ainihi a fannonin da suka zaɓa. Wadannan ƙwarewar ba wai kawai sun dace da tattalin arzikin Najeriya ba ne, har ma suna da gasa a matakin duniya. Muna ƙarfafa ‘yan ƙasa musamman mata, masu nakasa da matasa masu rauni da su amfana da wannan dama.”

Tare da kayan aiki da ma’aikata masu ƙwarewa da aka tanada, cibiyar na da niyyar yaye ɗalibai 16,000 a zangon horo na farko, tare da nufin cimma burinta na yaye ɗalibai 32,000 a kowace shekara.

Yace Gwamnatin Jihar Kaduna na kira ga al’ummar jihar da ma wajenta da su yi amfani da wannan dama don samun ƙwarewa da za ta basu damar samun aiki, kafa nasu sana’a, da dogaro da kai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Dumi-duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Ondo
Labarai

Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5

November 10, 2025
Matatun mai
Labarai

Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta 

November 10, 2025
Jibrin Kofa
Labarai

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

November 10, 2025
Next Post
Yaushe Mourinho Zai Koyar Da Kwallon Kafa A Kasashen Jamus Da Faransa?

Boko haram

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.