An yi kira ga jama’a masu aikin hakar ma’adanai a Jihar Kaduna da su yi rijista da gwamnatin Jihar domin samun gudanar da ayyukan su bisa ka’ida da doka.
Shugaban Kamfanin kula da hakar ma’adanai ta Jihar Kaduna Dakta Nura Sani Hussaini, shi ya yi wannan kiran a lokacin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a ofishin sa da ke Kaduna.
- Asalin Abin Da Ya Faru Game Da Dawowar ‘Yan Bindiga Hanyar Kaduna Zuwa Abuja – ‘Yansanda
- Bankin Duniya Ya Yi Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Nijeriya Da Kashi 3.3 A 2024
Dakta Nura Sani Hussaini ya kara da cewar kiran ya zama wajibi bisa ga la’akari da irin kalubale da hatsari da jama’a wadanda ba su yi rijista da gwamnati suke shiga ca yayin gudanar da aikin hakar ma’adanai a fadin Jihar.
Ya bada misali da iftila’in da ya faru kwanan nan a yankin Kaninkon dake karamar hukumar Jama’a inda aka samu asarar rayukan wasu mutane da ke aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, sannan ya kara da cewar hakan na ci gaba da faruwa sakamakon rashin bin doka da tsari da jama’ar da ke aikin hakar ma’adanai suke haifar wa.
Dakta Nura Sani Hussaini wanda ya bayyana cewar kofofin kamfanin nasu a bude suke ga dukkanin masu bukatar yin rijista da gwamnati domin aikin hakar ma’adanai a fadin Jihar gaba daya.
Shugaban ya yi kira ga dukkanin jama’ar jihar Kaduna da su sanya ido sosai akan masu aikin hakar ma’adanai domin da yawa wasu na aikin ba bisa doka ba inda ya ce duk lokacin da suka ga wani lamari da basu gamsu dashi ba su yi gaggawar sanar da Hukuma domin daukar matakan da suka dace.