Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamitin ba da shawara kan sabon albashin ma’aikata. Sa’o’i 48 kacal bayan da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000 kamar yadda aka yi sulhu tsakanin kungiyar kwadago da gwamnati.
Kano, ita ce jiha ta farko a fadin Nijeriya da ta kafa irin wannan kwamiti. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a yau a gidan gwamnatin jihar, wanda mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranta a madadin gwamnan.
- Gwamnatin Tarayya Na Ƙoƙarin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro – Ribadu
- Kiran Tada Hankali A Zanga-zanga: Rundunar ‘Yansanda Ta Cafke Wani Dan TikTok A Filato
A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, mai magana da yawun Mataimakin Gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya bayyana cewa, Gwamna Yusuf ya jaddada cewa, an dora wa kwamitin alhakin tsara yadda ya kamata a yi kan sabon mafi karancin albashin da aka amince da shi da kuma gabatar da wata shawara mai amfani don aiwatarwa ga gwamnatin jihar nan take.
Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa, aiwatar da sabon mafi karancin albashin zai kara habaka ci gaban jihar Kano a dukkanin bangarori, domin jin dadin ma’aikata shi ne abin da gwamnati ta sa gaba.
An dai dorawa kwamitin aikin bayar da sakamako cikin makonni uku. Gwamnan ya tunatar da ‘yan kwamitin cewa, an zabe su ne bisa cancanta, ya kuma bukace su da su bayar da gamsassun sakamako.
Sabon shugaban kwamitin da aka kaddamar shi ne, Alh. Usman Bala Muhammad, mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin jihar ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin jihar bisa amincewar da ta yi wa kwamitin.