Shugaban rundunar tsaro ta Sibin difen (NSCDC) na Jihar Kano, SC Muhammad Lawal Falala ya bayyana cewa sun hada kai da gwamnatin Kano domin samar da tsaro a makarantun jihar.
Ya ce sun yi wannan yunkuri ne bisa umarnin Gwamnatin tarayya na bai wa makarantun kasar nan kariya ta fuskar wayar da kai ga shugabanin makarantu, malamai da dalibai.
- Nazarin Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (15)
- ‘Yansanda Sun Cafke Wadanda Suka Kulle Matashi A Kejin Kare
A cewarsa, yunkurin na daga cikin aikin wannan hukuma na ba fararar hula kariya da hana lalata da satar kayayyakin amfani al’umma da dai sauransu.
Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan fitowarsa daga dakin taro na yini daya da aka shirya ga shugabanin makarantu, malamai da dalibai da kuma hadin gwiwar ma’akatar ilimi karkashin shugabancin, kwamishinan ilimi na Jihar Kano, Hon Umar Haruna Doguwa, wanda aka gabatar a kwalejin Sa’adatu Rimi a ranar Talata da ta gabata.
Shi ma a jawabinsa kwamishinan ilimi na Jihar Kano, Hon Haruna ya ba da tabbaci cewa ma’aikatar ilimi karkashin shugabancin Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a shirye take wajen ba da hadin kai na tabbatar da tsaro a makarantu da ma sauran wurare.
Jami’ai da suka wakilci hukumomin tsaro da suka hada da rundunar ‘yansanda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauransu sun gabatar da jawabi na hikimomi da dabaru da al’umma za su bai wajen tabbatar da tsaro a makarantu da sauran wurare. Inda mahalarta wannan taro suka nuna gamsuwarsu na wannan hadin gwiwa a tsakanin gwamnatin Kano da hukumar NSCDC.