Gwamnatin Jihar Kano na shirin yi wa yara 3,928,313 masu shekaru tsakanin kasa da 1 zuwa 5 allurar riga-kafi ta foliyo a zagaye na huɗu a Nuwamba 2025 da aka shirya farawa a ranar Asabar, 29 ga watan Nuwambar 2025.
Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Jihar Kano, Farfesa Salisu Ahmad, ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da Hukumar ta shirya tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA) da kuma abokan hulɗa na Shirin Kawar da Foliyo na Duniya (GPEI).
Ya ce, aikin yin riga-kafin zai ɗauki tsawon kwanaki huɗu, inda ake bi gida-gida da masallatai, da majami’u, wuraren kasuwanci, layuka, da wuraren kiwon lafiya.
Wanda ya samu wakilci daga Jami’in kula da canza halayyar zamantakewar ɗan adam na Hukumar, Nasir Kabir, Darakta Ahmad ya ce, jihar na da zimmar ganin nasarorin da aka samu wajen rage nau’in cutar Foliyo na 2 (cVPV2) da ke yaɗuwa ta ɗaure.














