Gwamnatin Jihar Kano, ta bayar da umarnin fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga karamar fadar jihar da ke Nassarawa.
Gwamnatin ta bai wa kwamishinan ’yansandan jihar, umarnin cewar za ta yi gyare-gyare a fadar.
- Ba Za’a Iya Warware Matsalar ‘Yan Gudun Hijira Ba In Har Wasu Kasashe Sun Ci Gaba Da Nuna Babakere
- Kotu Ta Rushe Dokar Da Ta Tsige Aminu Ado Bayero A Matsayin Sarkin Kano
Kwamishinan Shari’a kuma babban lauyan Jihar Kano, Barista Haruna Isa Dederi ne, ya bayar da wannan sanarwar yayin wani taron manema labarai da ya gudana a yau gidan gwamnatin jihar.
Wannan dai na zuwa ne bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke jihar ta yanke a yau dangane da dambaruwar masarautar Kano.
Kotun dai ta rushe dokar da ta tsige Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
Idan ba a manta ba majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar da gwamnatin Ganduje ta yi na samar da masarautu hudu gyara.
Daga bisani dokar kuma ta rushe masarautun, wanda daga bisani gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu a matsayin doka, tare da dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.