Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewar ta bayar da gudunmawar naira biliyan 2.5, domin kammala aiki ginin hanyoyin isa tashar Tsandauri.
Ta ce za a yi amfani da kudaden wajen kammala aikin hanyoyi da shingaye da hasken wutar lantarki da sauran abubuwan bukata a tashar Tsandaurin, domin samun tabbacin kammala aikin da gaggawa.
- Ko Makiyan Buhari Sun San Aikin Da Ya Yi Yafi Na Gwamnatocin Baya -Minista
- Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa
Kamar yadda Daraktan yada labaran ofishin mataimakin gwamnan Jihar Kano, Hassan Musa Fagge ya shaida wa manema labarai a Kano.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana haka ranar Juma’a lokacin da karamin ministan harkokin sufuri, Alhaji Mu’azu Jaji Sambo ya ziyarci shi a ofishinsa.
Ya ce Jihar Kano za ta tabbatar da ganin aikin ya kammala ta hanyar samar da kyakkyawan yanayi, kasancewar tashar za ta samar da ci gaban tattalin arziki ba kawai ga Jihar Kano ba har da kasa baki daya da wasu kasashe makwabta kamar irin su Nijar, Kamaro da kuma Chadi.
Da yake karanta jawabin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Dakta Gawuna cewa ya yi, Jihar Kano ce cibiyar ciniki da zuba hannun jari a arewacin Nijeriya, kuma ita ce ke da karfin tattalin arzikn da ba na man fetur ba da ya kai karfin dala biliyan 12, wacce take da damarmaki masu yawa ga masu zuba jari, don haka aikin zai kyautata amfanar albarkatun kasar da ke Jihar Kano wajen inganta rayuwar al’umma.
Ya kara da cewa hakan ya zama wajibi kasancewar darajar man fetur da kasar nan ta dogara da shi na kara faduwa.