Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin 8 ga Yuli, 2024 a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar kalandar Musulunci ta 1446 bayan hijira. Ya kuma ja hankalin al’umma da su yi amfani da hutun domin lissafi rayuwarsu a shekarar da ta gabata da kuma gudanar da ayyukan da za su taimaka wajen rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta a wannan mawuyacin lokaci.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnati na aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin karfafawa mutane gwiwa don dogaro da kai. Ya buƙaci al’ummar musulmi da su kara kaimi wajen gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a jihar.
- Kotu Ta Dage Shari’ar Matashin Da Ya Kone Masallata A Kano
- Binciken Ganduje: Kotu Ta Bai Wa Alkalan Kano Sa’o’i 48 Su Yi Murabus
Da yake bayyana ƙwarin gwuiwarsa, gwamnan ya bayyana cewa, bisa addu’o’i da goyon bayan al’umma, gwamnatinsa na da burin sauya fasalin jihar da kuma dawo da matsayinta na ɗaya daga cikin jahohin da suka fi samun ci gaban tattalin arziki a ƙasar nan.