Kotu ta dage shari’ar Shafiu Abubakar, wanda ake zargin ya yi sanadin mutuwar wasu masallata 19, a garin Gadan da ke karamar hukumar Gezawa a Jihar Kano.
An dage zaman ne sakamakon rashin kara sunayen mutanen da suka mutu sakamakon lamarin.
- Kenya Ta Dakatar Da Yi Wa Ma’aikatan Gwamnati Karin Albashi
- JAMB Ta Bankaɗo Ɗalibai 3000 Da Suka Kammala Karatun Bogi
Leadership ta ruwaito cewar cewa, matashin mai shekaru 38, mazaunin kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa, na fuskantar shari’a a babbar kotun Kano da ke Rijiyar Zaki.
Tun da farko dai an zargi Abubakar da cinna wa wani masallaci wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 14 tare da raunata wasu da dama.
Sai dai mai gabatar da kara, karkashin jagorancin daraktan masu gabatar da kara (DPP) na ma’aikatar shari’a ta Jihar Kano, Barista Salisu Tahir, ya sanar da kotun cewa adadin wadanda suka mutu ya karu daga 14 zuwa 19 saboda haka ya bukaci karin lokaci don sabunta takardar tuhumar.
Tahir ya ce “Muna neman wani kwanan wata don ba mu damar shigar da sabon sauyi don kara adadin wadanda abin ya shafa da kuma gabatar da shaidunmu a gaban kotu,” in ji Tahir.
A cewar masu gabatar da kara, Abubakar ya yi amfani da man fetur wajen cinna wa masallacin da ke kauyen Gadan wuta, a lokacin Sallar Asuba a ranar 15 ga watan Mayu, da misalin karfe 5:15 na asuba.
An garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da au Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
A cewar mai gabatar da karar, laifin ya saba da sashe na 336, 247, da 221 na dokar shari’a ta Jihar Kano.
Lauyar da ke kare wanda ake tuhuma, Barista Asiya Muhammad Imam, ta bukaci masu gabatar da kara da su gabatar da sabbin tuhume-tuhumen.
Daga bisani alkalin kotu, shari’a, Malam Halhalatul Huza’i Zakariyya, ya dage shari’ar zuwa ranar 18 da 19 ga watan Yuli, domin ci gaba da sauraren karar.