Gwamnatin Jihar Kano ta gano matsaloli a cikin tsarin albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi, inda aka gano ma’aikata 247 da suka yi ritaya ko kuma sun mutu, amma suna ci gaba da karɓar albashi.
Wannan bayani ya fito ne daga cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Musa Muhammad, ya fitar. A cewar sanarwar, wannan bincike ya gudana ne a yayin da ake gudanar da aikin tantancewa domin gyara tsarin albashin ma’aikatan gwamnati a jihar.
- Har Yanzu Da Akwai Jihohin Da Malaman Makaranta Ke Karbar Albashin Naira 18,000
- NLC Ta Yi Zanga-Zanga A Ofishin Wike, Ta Nemi A Biya Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Albashin N70,000
Sanarwar ta bayyana cewa, duk da cewa waɗannan ma’aikatan sun yi ritaya ko kuma sun mutu, sun kasance suna cikin jerin sunayen ma’aikatan da ke karɓar albashi, wanda hakan ya kai ga biyan kuɗi na ƙarya har Naira miliyan 27,824,395.40 a watan Maris na shekarar 2025 kawai.
Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa an dawo da wannan kuɗi zuwa asusun ƙananan hukumomi, kuma za a ci gaba da bincike don gano duk wanda ya yi wannan zamba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp