Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da duk wani tallace-tallacen magungunan gargajiya a fina-finan Hausa da masu tallar magunguna a lasifa a kan tituna.
Jami’in yada labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ya bayyana dalilin hukumar na yanke wannan hukunci da kin bin doka.
- EFCC Ta Miƙa Gidaje 750 Na Emefiele Da Ta Ƙwace Ga Ministan Gidaje
- Yanzu-yanzu: Tukunyar Gas Ta Fashe A Harabar Filin Wasannin Na Kasa Da Ke Gudana A Ogun
A cewar sanarwar, hukumar ta lura cewa, yawancin tallace-tallacen magungunan gargajiya da ake watsawa a bainar jama’a a kan tituna ko kuma wadanda aka sanya a cikin fina-finan Kannywood, ba a kawo mata don tantancewa da kuma amincewa da su ba.
Hukumar ta nanata cewa, dole ne a bayyana mata duk abubuwan da ke cikin tallatallace-tallace don tantancewa kafin a bayyanawa jama’a.
“Saboda haka, ana umurtar duk masu tallata magungunan gargajiya, masu fitar da Fina-finai, da masu shirya fina-finai da su daina watsa duk wani tallace-tallace a talabijin ko intanet har sai sun nemi izinin doka ta hanyar tantancewa,” in ji Sulaiman.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp