Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da karin kashi 50 cikin 100 na tallafin dalibai ‘yan asalin Jihar da ke karatu a makarantun cikin gida Nijeriya.
Majalisar ta kuma amince a fitar da Naira miliyan 865, 449,150.00 ga hukumar ba da tallafin karatu ta jihar a matsayin kudin tallafin don fara biyan daliban a fadin kananan hukumomi 44 karkashin masarautu biyar dake jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, wanda ya yi wa manema labarai karin haske kan hukuncin da majalisar ta Zartar a taronta na mako-mako a gidan gwamnatin, ya bayyana cewa adadin dalibai 40,494 ne za su ci gajiyar tallafin.
Ya kara da cewa, jimillar tallafin karatu ga daliban cikin gida guda 40, 494 daga masarautun Karaye da Bichi da Rano da Gaya da Kano a cikin kananan hukumomi 44 na jihar ya kai Naira MiliyanN836, 269, 150, yayin da za a kashe Naira Miliyan N29, 180, 000.00 Wajenn aiwatar da aikace-aikacen.