Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa yara 76 da aka kama yayin zanga-zangar #EndBadGovernance ga iyayensu. An gudanar da bikin miƙa yaran ne a yau Alhamis a Asibitin Muhammadu Buhari da ke Giginyu, Kano.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya tabbatar da cewa duk yaran sun samu kulawar lafiya kuma yanzu suna cikin koshin lafiya. Ya ce, “Sun warke bayan samun magani kuma yanzu suna da cikakkiyar lafiya. Ina tabbatar muku cewa gwamnati za ta ci gaba da kula da duk wanda ke bukatar taimako.”
- Sin Tana Fatan Raya Duniya Mai Adalci Dake Samun Bunkasuwa Tare Tsakanin Mabambantan Bangarori
- Gwamnatin Kano Ta Koka Kan Yawaitar Satar Magani A Asibiti
Haka kuma, Gidauniyar Bafarawa ta tallafa wa yaran da kuɗi ₦50,000 ga kowanne daga cikin su 76 domin su fara sabuwar rayuwa da sauƙaƙa musu komawa cikin al’umma. Yaran dai sun kasance a hannun Gwamnatin Kano tun ranar 5 ga Nuwamba, 2024, bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sallame su daga tuhumar cin amanar ƙasa da gwamnatin tarayya ta janye.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an ajiye yaran ne domin tabbatar da sun samu kulawar lafiya da gyaran halaye kafin a sake haɗa su da iyayensu.