Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar wa mazauna jihar cewa babu wata barazanar tsaro da ke tunkaro Kano a halin yanzu, tana mai jan hankalin jama’a da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta. Bayan taron kwamitin tsaron jihar da aka gudanar ranar Lahadi, hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa Kano na nan cikin kwanciyar hankali.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnati, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin, ya ce duk wasu rahotanni na matsalar tsaro da ake yaɗawa ba su da tushe, kuma babu wani sahihin bayanan sirri da yake nuna barazana ga zaman lafiyan jihar. Ya ce irin waɗannan bayanai marasa tabbas na iya haifar da fargaba a cikin al’umma.
- Barau Ya Gargaɗi Gwamna Abba Kan Siyasantar Da Batun Tsaro A Kano
- Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Sanarwar ta bayyana cewa dukkan hukumomin tsaro a jihar sun shiga shirin ko-ta-kwana, tare da tura jami’ai a sassa daban-daban don tabbatar da tsaro. Tofa ya ce gwamnatin jihar na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin leƙen asiri da aiyukan tsaro domin ƙarfafa haɗin kai da inganta tattara bayanan sirri a kan lokaci.
Gwamnatin ta shawarci jama’a da su kasance masu lura da abin da suke yaɗawa a kafafen sada zumunta, tare da gargaɗin cewa duk wanda aka kama yana yaɗa bayanan ƙarya zai fuskanci hukunci. Tofa ya tabbatar da cewa Kano na nan cikin aminci, kuma gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da gazawa ba.














