Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Litinin, 1 ga watan Agustan 2022 a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar Musulunci ta 1444 (bayan hijira).
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da haka cikin wata sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Laraba.
- Yau Alhamis Za A Yanke Hukunci Kan Malamin Da Ake Zargi Da Yi Wa Dalibarsa Kisan Gilla A Kano
- An Gano Wani Gurbataccen Taki Da Ake Sayar Wa Manoma A Kano
Gwamnan ya taya al’umar musulmai a jihar murnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci.
Gwamnan ya kuma nemi al’umar da su yi amfani da ranar hutun wajen rokon Allah da ya kawo saukin matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasar nan tare da rokon ci gaban tattalin arzikin jihar da ma kasa baki daya.
Abdullahi Ganduje, ya kuma nanata aniyar gwamnatinsa na ci gaba da sauke alkawuran da ta dauka na inganta rayuwar al’umar jihar ta hanyar gudanar da tsare-tsaren da shirye-shiryen masu alfanu kai tsaye ga rayukan jama’a.
Kazalika Gwamnatin ta yi amfani da wannan damar wajen kira ga wadanda har yanzu da basu mallaki katin shaidar yin zabe ba da su yi hakan domin samun damar zaben wadanda suke so a yayin babban zaben 2023 da ke tafe.
A dai ranar Asabar 30 ga watan Yulin 2022 ne ake sa ran shiga sabuwar shekarar Musulunci.