Gwamnatin Jihar Kano, ta sassauta dokar hana fita daga karfe 8 na safe zuwa karfe 2 na rana a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Baba Halilu Ɗantiye ne, ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.
- Wakilin CMG Ya Zanta Da Shugaban Kasar Timor-Leste
- An Harbi Mutane 8, 4 Sun Mutu A Zanga-Zanga A Kano
Sanarwar, ta bayyana cewa sassaucin dokar zai fara daga gobe Lahadi da misalin karfe 8 na safe zuwa ƙarfe 2 na rana don jama’a su samu su gudanar da harkokinsu a tsakanin wannan lokacin kafin komai ya daidaita.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin ta sanya dokar hana fita biyo bayan tashe-tashen hankula da aka samu a lokacin zanga-zangar yunwa a ranar Alhamis a jihar.
An fara zanga-zangar ne a fadin Nijeriya don nuna fushi kan halin da kasar ke ciki game da tabarbarewar tattalin arziki da kuma tashin gwauron zabin kayan abinci.