Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftace muhalli na watan Afrilu domin bai wa ɗalibai damar zana jarabawar JAMB cikin sauƙi ba tare da wata tangarɗa ba.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dokta Dahiru Hashim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da kan Jama’a na ma’aikatar, Isma’il Gwammaja, ya fitar.
- ‘Yansanda Sun Damƙe Mutane 148, Sun Ƙwato Makamai A Adamawa
- Tallafa Wa Al’umma: Ya Dace Gwamnoni Su Yi Koyi Da Jihar Zamfara – UNDP
Ya ce an yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ka da hakan ya haifar wa ɗaliban da ke rubuta jarabawar JAMB a faɗin ƙasar nan cikas.
Dokta Hashim ya ƙara da cewa aikin tsaftace muhalli zai ci gaba kamar yadda aka saba a watan Mayu 2025.
Ya kuma roƙi al’umma da su fahimci wannan mataki, su kuma guji zubar da shara a wuraren da ba su dace ba.
Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsafta domin tabbatar da tsaftar muhalli a jihar.
Aikin tsaftar muhalli na wata-wata, wanda ake yi a ƙarshen kowane wata, ana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wasu awanni domin tsaftace muhalli a faɗin Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp